Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-14 13:06:43    
Kwamitocin wasannin Olympic da 'yan wasanni na wadansu kasashe sun nuna rashin amincewarsu da yin adawa da wasannin Olympic na Beijing

cri
Kwanakin nan, kwamitocin wasannin Olympic da 'yan wasanni na kasashen Cuba, da Canada, da Faransa, da Poland, da dai sauransu sun bayyana bi da bi cewa, sun nuna rashin amincewarsu da yin adawa da wasannin Olympic na Beijing, ko kuma kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympics ta hanyar nuna karfin tuwo, za su tura yan wasa zuwa wasannin Olympic na Beijing.

A ran 12 ga wata a birnin Havana, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Cuba Mr. Jose Ramon Fernandez ya bayyana cewa, kasar Cuba ta sake yi watsi da ko wane yunkurin adawa da wasannin Olympic na Beijing, da kuma kare ikon kasar Sin na shirya wasanin Olympic ba a karkashin matsin lamba ba.

Jami'in kwamitin wasannin Olympic da wakilan yan wasanni na kasar Canada kuma sun nuna adawa da a sanya siyasa a cikin wasannin Olympic, kuma sun yi Allah wadai da farmaki da 'yan a-ware na Tibet suka kai wa wutar wasannin Olympic.

A ran 12 ga wata, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Faransa Mr. Henri Serandour ya bayar da labari a jaridar "Le Monde" cewa, ya yi bakin ciki da kuma fushi sabo da cikas da aka kaiwa ga aikin mika wutar wasannin Olympic a birnin Paris, kuma ya yi kira da kada a bata burin yan wasanni domin siyasa.

Ban da wannan kuma, mutane da abin ya shafa na kasashen Sweden, da Hungary, da Iran, da Poland da dai sauran kasashe sun bayana ra'ayoyinsu na nuna rashin amincewarsu da yin adawa da wasannin Olympic na Beijing. (Zubairu)