Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-14 11:48:57    
Wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta isa Muscat

cri
Da sanyin asubar yau 14 ga wata, da misalin karfe 5 da minti 20, agogon wurin, jirgin saman musamman dauke da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ya isa babban birnin kasar Oman wato Muscat daga Dar es Salaam, hedkwatar kasar Tanzaniya, inda za a fara yin bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing na zango na 9.

Ministan harkokin motsa jiki, kuma shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na Oman Ali Bin Masoud, da babban mai daidaita bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a Muscat, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na kasar Habib Maki sun taryi Liu Jingmin, mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing mai dauke da wutar gasar wasannin Olympics a filin jirgin sama, jakadan Sin a Oman Pan Weifang shi ma ya halarci bikin maraba.

Bisa labarin da muka samu, an ce, za a fara yin bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a yau, da misalin karfe 5 da maraice, agogon wurin. Za a fara zagayawa da wutar daga jirgin ruwa mai suna Suhar a tsibirin Bustan na birnin Muscat, kuma a lambun shan iska na Al-qurm ne za a shirya bikin kawo karshen aikin zagayawa da wutar a kasar. Bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a Muscat zai samu halartar masu rike da wutar guda 80. A yau, mutanen Oman za su sanya tufafin gargajiya domin maraba da zuwan wutar gasar wasannin Olympics.

Bayan da za a kammala bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a kasar Oman yau, gobe ranar 15 ga wata, wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta tashi zuwa babban birnin Pakistan wato Islamabad.(Murtala)