Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-14 10:14:15    
Wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta tashi daga Dar es Salaam zuwa Muscat

cri
Bayan da aka kammala bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara a babban birnin Tanzaniya wato Dar es Salaam, jirgin saman musamman dauke da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 ya tashi daga Dar es Salaam zuwa Muscat, hedkwatar kasar Oman wadda ita ce zango na 9 na wannan gagarumin bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a ketare.

Da daren shekaranjiya wato ranar 12 ga wata, agogon wurin, wutar gasar wasannin Olympics ta tashi daga babban birnin kasar Argentina wato Buenos Aires, daga baya ne ta isa birnin Dar es Salaam dake gabashin Afirka, inda aka yi bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a jiya 13 ga wata da yamma. Da misalin karfe 3 da yamma, agogon wurin, mai zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta karshe, wato mataimakiyar sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, kuma daraktar gudanarwa ta hukumar kula da mazaunan 'yan Adam ta MDD Madam Anna Tibaijuka ta kammala aikin mika wutar, haka kuma ta kunna wuta a tukunyar wutar gasar wasannin Olympics. Wannan dai ya alamanta cewar an kammala aikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara a wannan zango.

Dar es Salaam ta kasance zango na 8 a duk duniya inda aka zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing. An soma wannan aiki ne a tashar jirgin kasa ta hanyar dogo dake tsakanin Tanzaniya da Zambiya, an kuma kammala wannan aiki ne a filin wasannin motsa jiki na kasar Tanzaniya, wanda kasar Sin ta tallafawa Tanzaniya wajen gina shi. Tsawon hanyar da aka bi wajen zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a Tanzaniya ya kai kilomita 5. Masu rike da wutar yola guda 80, wadanda suka zo daga Sin, da Tanzaniya, da sauran kasashen Afirka sun halarci bikin.(Murtala)