Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-12 21:29:47    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da firaminista Kevin Rudd na Australia da firaminista Fredrik Reinfeldt na Sweden

cri
A ran 12 ga wata a lardin Hainan na kasar Sin, shugaba Hu Jintao na kasar ya gana da firaminista Kevin Rudd na Australia da firaminista Fredrik Reinfeldt na Sweden bi da bi.

Yayin da Mr. Hu Jintao ke ganawa da firaminista Kevin Rudd na Australia ya bayyana cewa, harkokin jihar Tibet harkokin gida ne na kasar Sin. Mr. Kevin Rudd ya nanata cewa, kasar Australia ta amince da mallakar kan kasar Sin ga Tibet da Taiwan sosai, kuma yana fatan za a samu cikakkiyar nasara wajen shirya wasannin Olimpic na Beijing.

Yayin da Mr. Hu Jintao ke ganawa da firaminista Reinfeldt na kasar Sweden kuma ya bayyana cewa, bangaren Sin yana son hadin kai a tsakaninsa da bangaren Sweden, kuma za su kara karfin hadin gwiwa daga fannoni daban-daban, da kara samun ci gaba wajen dangantakar da ke tsakanin kasashen 2. Mr. Reinfeldt ya bayyana cewa, shirya wasannin Olinpic na Beijing tare da nasara yana da muhimmancin gaske ga kasar Sin, haka ga Asiya da duk duniya baki daya, ina fatan za a samu nasara wajen shirya wasannin Olimpic na Beijing. (Umaru)