Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-12 19:07:14    
Batun Tibet harkar gida ce ta kasar Sin, kuma dinkuwar kasa ko jawo baraka ga kasa sabani ne da ke tsakanin gwamnatin Sin da Dalai Lama, in ji shugaban kasar Sin, Hu Jintao

cri
Yau shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya bayyana cewa, Batun Tibet harkar gida ce ta kasar Sin. Sabanin da ke tsakanin gwamnatin kasar Sin da rukunin Dalai Lama ba maganar kabila ko ta addini ko kuma ta hakkin bil Adam ba ce, a maimakon hakan dai, shi batu ne na kiyaye dinkuwar kasa da kuma jawo baraka ga kasa.

Mr.Hu Jintao ya yi wannan kalami ne a lokacin da yake zantawa da firaministan kasar Australia, Kevin Rudd a birnin Sanya na kasar Sin.

A game da aukuwar tarzoma a binrin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, abin ba wai "zanga zanga cikin lumana" kamar yadda wasu suka fada ba, amma laifi ne na nuna karfin tuwo. Game da irin wannan laifi na lalata hakkin bil Adam da zaman al'umma da kuma kawo manyan illoli ga rayukan jama'a da dukiyoyinsu, kowace gwamnati ba za ta zauna ta yi kallo kawai ba.

Mr.Hu Jintao ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na bude kofarta ga Dalai Lama wajen yin shawarwari. Yanzu Dalai Lama ne ke kawo cikas ga shawarwarin a maimakon mu. Muddin bangaren Dalai Lama ya daina ayyukan jawo baraka ga kasar Sin da nuna karfin tuwo da kuma lalata wasannin Olympics na Beijing, to, muna son ci gaba da shawarwari da shi ko da yaushe.

Daga Nasa bangaren kuma, Mr.Kevin Rudd ya jaddada cewa, Australia na amincewa da mulkin kan kasar Sin a Tibet da Taiwan, kuma ba za ta canza manufarta ta kasancewar Sin daya tak a duniya ba.(Lubabatu)