Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-12 20:15:58    
Magajin garin birnin Dares Salam ya yi Allah wadai da kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympics da aka yi

cri
A ran 13 ga wata, za a fara mika wutar wasannin Olympics na Beijing a birnin Dares Salam, babban birnin kasar Tanzania. A jiya 11 ga wata, magajin garin birnin Dares Salam, Adam Kimbisa ya yi Allah wadai da kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympics da wasu suka yi a kwanan baya. Ya kuma bayyana cewa, mika wutar wasannin Olympics zai sa kaimi ga bunkasuwar al'adu da tattalin arziki na Tanzania.

Mr.Kimbisa ya ce, mika wutar wasannin Olympics kasaitaccen biki ne na duk duniya. Kamata ya yi a hukunta duk wadanda suka nemi kwace wutar yola ta wasannin Olympics da kuma lalata ta. Ya ce, kasancewar Dares Salam birni kawai a nahiyar Afirka da aka zabe shi wajen mika wutar wasannin Olympics, mazaunan birnin na jin alfahari sosai. Yanzu sassa daban daban na Dares Salam a shirye suke, kuma jama'a na cike da farin ciki, har ma sun shirya bukukuwa iri iri don nuna maraba ga wutar. (Lubabatu)