Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-12 20:14:47    
Sabon shugaban AU ya nuna tsayayyiyar adawa ga yunkurin neman lalata wasannin Olympics

cri
Jiya 11 ga wata, shugaban kasar Tanzania kuma sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Jakaya Mrisho Kikwete ya bayyana cewa, yanzu akwai wasu mutanen da ke yunkurin neman lalata wasannin Olympics, a dangane da haka, jama'ar Tanzania da na kasashen Afirka baki daya na nuna tsayayyiyar adawa ga yunkurin, kuma suna cike da imani da cewa, za a cimma cikakkiyar nasarar gudanar da wasannin Olympics na Beijing.

A ran nan, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya yi shawarwari tare da shugaba Kikwete a birnin Sanya na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, kuma Mr.Kikwete ya yi wannan furuci ne a gun shawarwarin. Mr.Kikwete ya bayyana cewa, Tanzania na farin ciki sosai da zama kasar da aka yada zango wajen mika wutar wasannin Olympics na Beijing, kuma za ta yi iyakacin kokarin neman cimma cikakkiyar nasarar bikin mika wutar, ko kadan ba za ta yarda da kawo cikas ga bikin ba.(Lubabatu)