Jiya 11 ga wata da dare, jirgin saman da ke dauke da wutar wasannin Olympics ta Beijing, ya tashi daga birnin Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina zuwa birnin Dares Salam, babban birnin kasar Tanzania, wanda zai kasance zango na 8 a kan hanyar mika wutar wasannin Olympics ta Beijing.
Birnin Buenos Aires ya kasance zango na 7 a kan hanyar mika wutar wasannin Olympics ta Beijing, kuma a birnin, aka shafe tsawon awa biyu da rabi ana wannan biki na mika wutar wasannin Olympics ta Beijing.
A ran 13 ga wata, za a fara mika wutar wasannin Olympics a birnin Dares Salam.(Lubabatu)
|