A ran 12 ga wata, jami'in kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi jawabi kan kudurarren shirin da majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartar na sa hannu cikin harkokin jihar Tibet da yin adawa da kasar Sin, ya yi matukar fushi da rashin amincewa sosai ga majalisar wakilai ta Amurka sabo da ta yi biris da kiyewa sosai da matsalokin da hukumar Sin ta gabatar mata cikin rashin jin dadi, kuma ta zartas da shirin kudurin da Nancy Pelosi, shugabar majalisar ta gabatar na tsoma baki cikin harkokin jihar Tibet da yin adawa da kasar Sin.
Wannan jami'i ya bayyana cewa, wannan shirin kuduri ya yi watsi da hakikanan abubuwa na gaskiya, kuma ya yi biris da dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma ya kai suka ba gaira ba dalili kan gwamnatin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin wadda ta daidaita tarsomar da ta barke a Lhasa bisa doka, kuma ya shiga sharo ba shanu a cikin harkokin gida na kasar Sin, ya bakanta ran jama'ar Sin kwarai.
Wannan jami'i ya ci gaba da cewa, mummunan tashin hankali da aka haddasa a birnin Lhasa wanda rukunin Dalai Lama shi ne ya yi kulle-kulle da yin shiri da kuma hura wutar yin sa, kuma ya kirkiro ta hanyar gama kai da 'yan aware masu neman 'yancin kan Tibet da ke cikin kasar Sin da na waje da ita, sun yi haka ne duk domin bakin nufinsu na tada rikici, da kebantar da jihar Tibet daga kasar Sin, da jawo cikas ga zaman rayuwa mai jituwa da jama'ar Tibet ke yi yadda ya kamata, da jawo illa ga wasannin Olimpic na Beijing, amma ko kusa ba kamar abubuwan da rukunin Dalai Lama ke yin kururuwa na wai yin zanga-zangar zaman lafiya da 'yan kabilar Tibet na cikin kasar da na waje da ita suka yi bisa radin kansu ba, ballantana ma yana da nasaba ga matsalar hakkin dan adam da 'yancin bin addini da kuma kiyaye al'adu. (Umaru)
|