Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 21:43:24    
Dalai Lama na ci gaba da yaudarar jama'a, in ji sharhin kamfanin dillancin labarai na Xinhua

cri
Yau kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar da sharhin cewa, bayan aukuwar tarzoma a birnin Lhasa, Dalai Lama na kokarin barbaza karyarsa da kuma boye gaskiya. Ko da yake an sha tone karyarsa, amma yana ci gaba da yaudarar jama'a.

Kwanan nan, Dalai Lama ya kai ziyara a wasu kasashe bisa tutar yin jawabi. A ran 10 ga wata, a gun taron manema labarai da ya kira a kasar Japan, ya ce, "ba ya adawa da kasar Sin", kuma "tun farkon fari yana nuna goyon baya ga wasannin Olympics da Beijing za ta gudanar".

Sharhin ya ce, a cikin shekaru kusan 50 da suka wuce, mabiyan Dalai Lama sun yi iyakacin kokarin jawo baraka ga kasar Sin. Tun farkon fari, 'yan awaren Tibet da ke karkashin jagorancin Dalai Lama suna kokarin lalata wasannin Olympics da kuma kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympics a duk duniya da ake yi, ko nuna karfin tuwo da kwace wutar yola ta wasannin Olympics sun kasance hanyar da Dalai Lama ke bi wajen nuna wasannin Olympics na Beijing? (Lubabatu)