Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:54:52    
'Dan majalisar Turai na kasar Romania ya la'anci matsayin da majalisar ke dauka kan batun Tibet

cri
Jiya 10 ga wata a birnin Brussels, Mr. Adrian Severin, 'dan majalisar Turai daga jam'iyyar dimokuradiya ta zaman al'umma ta kasar Romania, ya bayyana cewa, kudurin da majalisar Turai ta zartas game da halin da Tibet ke ciki na manufanci, da maras hangen nesa, da kuma ba sauke nauyin da ke bisa wuyanta ba.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Rompres ya bayar an ce, majalisar Turai ta yi fatali da hakikanin hali, wato masu neman 'yancin kan Tibet sun yi aikace-aikace ba bisa doka ba, da kuma matsayin da kullum kasar Sin ke dauka, ta shirya cikakken taro a wannan rana a birnin Brussels, kuma ta zartas da kudurin da 'yan majalisar da ke adawa da kasar Sin suka gabatar kan halin da Tibet ke ciki, inda ta bukaci M.D.D. da ta kafa wata karamar kungiyar bincike ta 'yancin kai, da kuma aika da ita zuwa Tibet don yin bincike, bayan haka kuma, ta yi kira ga kasashen Turai da su dauki matsayi iri daya kan batun nuna adawa da bikin bude wasannin Olympics.

Bayan taron, Mr. Severin ya bayyana wa manema labaru cewa, zartas da wannan kuduri ya nuna cewa, wasu 'yan majalisar Turai sun mayar da batun hakkin bil Adam kamar harkar siyasa. Kuma ya ce, kudurin zai kara gurfuntacciyar dangantaka a tsakanin Turai da Sin. (Bilkisu)