Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:44:07    
Wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya yi godiya ga jama'ar kasashe daban daban da suka nuna goyon baya ga wutar yola ta wasannin Olympics

cri
Jiya 10 ga wata, wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympics na birnin Beijing, ya yi jawabi kan ayyukan mika wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing. Inda ya yi godiya ga kasashe, da birane da kuma jama'ar da wutar yola ta wuce, a waje daya kuma, ya jaddada cewa, ayyukan mika wutar ya gamu da cikas da masu neman 'yancin kan Tibet suka kawo, haka kuma mutanen da ke kaunar kyakkyawan tunanin Olympics na dukkan duniya sun la'ancin wannan.

Wannan jami'i ya ce, an soma mika wutar yola ta wasannin Olympics ta Beijing daga ranar 1 ga watan Afril a kasashen ketare, kuma ta gamu da kulawa da goyon baya daga kasashe da biranen da ta wuce. Amma, masu neman 'yancin kan Tibet kadan sun kawo cikas ga ayyukan mika wutar yola. Saboda haka, gaba daya Sinawa da ke gida da na waje sun la'anci haka.

Bugu da kari kuma, wannan jami'i ya ce, kasar Sin ta shirya wasannin Olympics bisa matsayinta na kasa mai tasowa, za ta bi ka'idoji da bukatun da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya yi, da kuma koyon fasahohi daga kasashen da suka taba daukar nauyin shirya wasannin Olympics, an yi imani cewa, a karkashin goyon bayan da kwamitin wasannin Olympics na duniya, da kwamittocin wasannin Olympics na kasashe da shiyyoyi daban daban, da kuma 'yan babban iyalin Olympics suka bayar, ko shakka babu, birnin Beijing zai shirya wasannin Olympics na shekarar 2008 cikin nasara. (Bilkisu)