Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:36:30    
Mr Samaranch ya yi adawa da a yi amfani da gasar wasannin Olympics domin cim ma burin siyasa

cri

A yayin da yake amsa tambayoyin da kafofin watsa labaru na kasar Spain suka yi masa, shugaba mai girmamawa na kwamitin gasar wasannin Olympics na duniya Mr Juan Antonio Samaranch ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga duniya bayan da ta shirya gasar wasannin, ya yi adawa da a yi amfani da gasar wasannin Olympics domin cim ma burin siyasa.

Mr Samaranch ya yaba da ayyukan share fage da birnin Beijing yake gudanarwa domin gasar wasannin Olympics. Ya ce, ya ga babban canjin da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 30 da suka wuce. Kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar tattalin arziki, farar hula sun fi samun moriya daga hakan. A sa'i daya kuma, ya yi imani cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga duniya bayan gasar wasannin Olympics. Mr Samaranch ya ci gaba da cewa, kamata ya yi kasashen da ba su girmama hakkin 'dan Adam na sauran kasashe su tuna da kuskurensu, bai kamata ba su yi amfani da gasar wasannin Olympics domin cim ma burin siyasa.(Danladi)