Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:01:05    
Aikin mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing zai daukaka fahimtar juna a tsakanin jama'ar Sin da Tanzania

cri
Tun bayan watan Mayu na shekarar bara da aka tabbatar da birnin Dar Es Salaam, hedkwatar kasar Tanzania da ya zama birnin da za a gudanar da aikin mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, ofishin jakadanci na kasar Sin a Tanzania ya himantu wajen share fagen aikin. A ran 13 ga wata, za a mika wa wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Dar Es Salaam. A kwanan baya, wakilinmu ya zanta da Liu Xinsheng, jakadan kasar Sin a Tanzania.

Domin maraba da wutar wasannin Olympic, a cikin watanni 10 da suka wuce, a karkashin jakada Liu, dukan ma'aikatan ofishin jakadanci na kasar Sin a Tanzania sun yi hadin gwiwa da bangaren Tanzania, sun kuma taimaka wa juna sosai wajen gudanar da dimbin ayyukan share fage. Dar Es Salaam, birni ne kawai na Afirka da za a yi aikin mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, shi ya sa ya jawo hankulan kasashen duniya sosai.

Jakada Liu ya yi karin bayani da cewa,'Wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta ratsa kasashe 19 na duniya, a Afirka kuma, sai Dar Es Salaam kawai. Tanzania, wata muhimmiyar kasa ce da ke gabashin Afirka, kuma aka tabbatar da kwanciyar hankali ta fuskar siyasa da kyakkyawar odar zaman al'ummar kasa da kuma jituwa a tsakanin kabilu. A matsayinta na hedkwatar kasar, Dar Es Salaam tana cikin wurin taswira mai kyau, an fi dora muhimmanci kan raya ta. Mazauna wurin na da kirki sosai, sun kuma nuna wa jama'ar Sin zumunta sosai. Sun sha yin kokarin samun damar gudanar da aikin mika wa juna wutar, a karshe dai sun sami amincewa daga kwamitin wasannin Olympic na duniya. Wannan ya nuna zumuncia a tsakanin jama'ar Tanzania da Sin, haka kuma ya nuna kaunar da jama'ar Tanzania ke nunawa kan zaman lafiya da wasannin motsa jiki.'

Lalle, a cikin goman shekaru da suka wuce, kasashen Sin da Afirka sun jure wahalhalu wajen raya huldar zumunci da hadin gwiwa a tsakaninsu. Jakada Liu ya ci gaba da cewa,'Za a mika wa juna wutar wasannin Olympic a Dar Es Salaam a ran 13 ga wata. Dukanmu muna ganin cewa, wannan zai samar wa jama'ar kasashen 2 kyakkyawar damar kara fahimtar juna, haka kuma, zai sanya jama'ar Tanzania su kara saninsu kan ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing da bunkasuwar kasar Sin da al'adun Sin da jama'ar Sin. Sa'an nan kuma, jama'ar Sin za su kara saninsu kan bunkasuwar Tanzania a harkokin tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, da al'adu da muhallin halittu da ni'imtattun wurare na Tanzania.'

Jakada Liu ya kan mai da hankali sosai kan sauraren ra'ayoyin mutanen Tanzania kan mika wa wutar gasar wasannin Olympic a kasarsu a lokacin da yake gudanar da aikinsa na yau da kullum, Mr. Liu ya ce,'Dukan jami'an gwamnatin da mutanen rukunin wasannin motsa jiki da fararen hula na Tanzaniya suna zura ido kan mika wa juna wutar wasannin Olympic a kasarsu, suna ganin cewa, wannan zai kasance dama mai kyau wajen yada ruhun wasannin Olympic da kara sani kan kasar Sin. Dukansu suna alla-alla wajen nuna goyon baya da kuma ba da gudummowa domin samun nasarar mika wutar wasannin Olympic.'

Baya ga mutanen Tanzania, Sinawa 'yan kaka gida da ke zama a Tanzania su ma suna zura ido kan wutar wasannin Olympic, Mr. Liu ya ce,'Mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Dar Es Salaam ya faranta wa Sinawa 'yan kaka gida da ke zama a Tanzania rai sosai. Suna ganin cewa, wannan yana da muhimmanci sosai ga kasar Sin, wadda ke samun bunkasuwa sosai. Suna maraba da wutar da hannu biyu biyu, ban da wannan kuma suna shiga harkokin maraba da wutar cikin himma.'

Mr. Liu ya bayyana cewa, saboda ofishin jakadanci na kasar Sin a Tanzania ya yi shawarwari da bangaren Tanzania cikin himma, shi ya sa ana gudanar ayyukan share fage yadda ya kamata, yanzu ayyukan share fagen mika wa wutar wasannin Olympic a Dar Es Salaam a shirye suke.(Tasallah)