Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 18:54:08    
(Sabunta) Wutar lantarki ta wasannin Olympics ta isa birnin birnin Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina

cri

A ran 10 ga wata da yamma bisa agogon wurin, wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2008 ta isa birnin Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina. Kuma wannan shi ne karo na farko da za a mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics a kasar.

A ran 10 ga wata da karfe 5 da yamma bisa agogon wurin, jirgin sama na musamman da yake dauke wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ya isa filin jirgin sama na Ezeiza na birnin Buenos Aires. Zeng Gang, jakadan Sin da ke kasar da kuma Madam Alicia Masoni de Morea, mataimakiyar shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar da kuma wakilan gwamnatin kasar kusan 100 sun je filin jirgin sama don yin marhabin da wutar.

A wannan rana kuma, shugabar kasar Argentina CristinaFernandez de Kirchner ta gana da jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Argentina a fadar shugaba, inda ta bayyana cewa, ko shakka babu aikin mika wutar yolar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Buenos Aires zai ci nasara, a sa'i daya kuma ta nuna fatan alheri ga birnin Beijing da ya shirya gasar cikin nasara.
Birnin Buenos Aires birni ne daya tak na nahiyar Amurka ta Kudu da za a mika wutar gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008 a ciki. Za a kaddamar da mika wutar daga ran 11 ga wata da karfe 2 da yamma bisa agogon wurin. (Bilkisu)