Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 16:45:37    
Kasar Niger ta yi adawa da a sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Daga ranar 1 zuwa 10 ga wata a birnin Beijing, shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na kasar Niger wato Mr Mohamed Talata Dula ya halarci taron wakilai na karo na 16 na kananan kungiyoyin gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, da kuma babban taro na 10 na kwamitin daidaita harkokin gasar wasannin Olympics ta 29 ta kungiyar gasar wasannin Olympics ta duk duniya. Bayan tarurrukan biyu, Mr Dula ya ce, kwamitin gasar wasannin Olympics na kasar Niger ya yi adawa da a sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics, kasar Niger za ta nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Ya ce,

'Ba mu so a sa siyasa cikin wasanni, don in a sa siyasa, yara masu yin sport ba su ji dadi, za a kashe sport. Ya kamata dukkan mutane su zauna tare, suka sa karfinsu tare, a zo a yi wasan nan.'

Mr Mohamed Talata Dula ya ci gaba da cewa,

'Har yanzu, ban ji mutanen Niger ba su zuwa wannan wasa ba, muna aiki, mu yi dukkan abun da muke iya, domin mu zo abin nan wasa.'

Ban da wannan kuma, Mr Mohamed Talata Dula ya yaba da aikin share fage da birnin Beijing yake yi, ya ce, bai fuskanci ko wace matsala ba a Beijing, birnin Beijing yana gudanar da ayyuka masu kyau a fannonin ingancin iska da abinci da otel da dai sauransu, kasar Niger za ta nuna goyon baya sosai ga gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)