Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 15:25:40    
Wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta isa birnin Buenos Aires

cri

A ran 10 ga wata da yamma bisa agogon wurin, wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2008 ta isa birnin Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina. Kuma wannan shi ne karo na farko da za a mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics a kasar.

A ran 10 ga wata da karfe 5 da yamma bisa agogon wurin, jirgin sama na musamman da ya dauke wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ya isa filin jirgin sama na Ezeiza na birnin Buenos Aires. Zeng Gang, jakadan Sin da ke kasar da kuma Madam Alicia Masoni de Morea, mataimakiyar shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar da kuma wakilan gwamnatin kasar kusan 100 sun je filin jirgin sama don yin marhabin da wutar.

Birnin Buenos Aires birni ne daya tak na nahiyar Amurka ta Kudu da za a mika wutar gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008 a ciki. Za a kaddamar da mika wutar daga ran 11 ga wata da karfe 2 da yamma bisa agogon wurin.(Kande Gao)