Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 13:55:42    
Tanzaniya tana begen zuwan wutar yola

cri

Za a yi aikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Dares Salam, birni mafi girma na kasar Tanzaniya a ran 13 ga wata. Ran 10 ga wata, babban sakataren kwamitin wasannin Olympic na kasar Tanzaniya Filbert Bayi ya karbi ziyarar musamman da manema labarai suka yi masa, inda ya bayyana cewa, sun riga sun gama dukkan ayyukan share fage domin yin maraba ga wutar yola ta Beijing, kuma suna begen zuwanta a nahiyar Afirka sosai da sosai.

Bayi ya ce, ma'anar Dares Salam a cikin harshen Bantu na Afirka da kuma Larabci 'tashar zaman lafiya' ce. Babban batun aikin mika wutar yola ta Beijing 'tafiyar zaman jituwa' ne, ma'anarsa 'tafiyar zaman lafiya' ce, ana iya cewa, babban batun aikin da ma'anar birnin Dares Salam duk daya ne. Bayi ya ci gaba da cewa, gasar wasannin Olympic bikin wasannin motsa jiki ne mai ma'anar aminci da zaman lafiya, shi ya sa gasar wasannin Olympic muhimmin lokaci ne wajen hada kan duk duniya. Aikin mika wutar yola ya bude wannan gaggarumin biki. Saboda haka hukumar Tanzaniya ba ta yarda da sa siyasa a cikin aikin ba. Bayi ya ce, a halin da ake ciki yanzu, sassan da abin ya shafa daban daban na kasar Tanzaniya suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma sun shirya sosai wajen maraba da zuwan wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing. (Jamila Zhou)