Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 13:16:03    
Bangaren kasar Sin ya nuna fushi da tsayayyiyar adawa ga kudurin da Majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartas don yin adawa da Sin bisa batun Tibet

cri
A ranar 11 ga wannan wata, kakakin majalisar harkokin kasa ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayar da jawabi a kan kudurin yin adawa da kasar Sin da Majalisar wakilai ta kasar Amurka ta yi bisa batun Tbiet, inda ta bayyana cewa, kudurin ya rikitar da tarihi da hakikanan abubuwa na Tibet kiri da muzu, kuma ta yi shishigi cikin harkokin kasar Sin ba ji ba gani, bangaren kasar Sin ya nuna fushi da tsayayyar adawa sosai ga kudurin.

Madam Jiang Yu ta bayyana cewa, a ranar 9 ga watan Afril, majalisar wakilai ta majalisun kasar Amurka ta yi biris da matsayin da kasar Sin ta dauka da gaske, ta dudduba kuma ta zartas da kudurin yin adawa da kasar Sin da shugaban majalisar Nancy Pelosi ta gabatar dangane da batun Tibet kiri da muzu. Kudurin ya rikitar da tarihi da hakikanan abubuwa na Tibet, kuma ta kai suka kan gwamnatin jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokinta na kanta ba gaira ba dalili saboda ta daidaita lamarin da aka yi laifufuka da karfin tuwo a jihar , wannan ne shishigi ne da ta yi wa harkokin gida na kasar Sin ba ji ba gani, kuma ta bata ran jama'ar kasar Sin sosai, bangaren kasar Sin ya nuna fushi da tsayayyar adawa sosai a kan wannan.

Madam Jiang Yu ta ci gaba da bayyana cewa, muna neman Majalisun kasar Amurka da su girmama hakikanan abubuwa, su banbanta gaskiya da maras gaskiya, kuma nan da na su dakatar da maganganunsu na kuskure na yin shishigi cikin harkokin kasar Sin da kawo lahani ga dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka.(Halima)