Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 12:50:54    
Wasu kasashe da gwamnatocinsu da manyan mutanensu sun nuna adawarsu ga dagiyar da aka yi wa wasannin Olimpic

cri
Kwanan baya, wasu kasashe da gwamnatocinsu da manyan mutanensu sun nuna adawarsu ga dagiyar da aka yi wa wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008, kuma sun yi adawa da mayar da wasannin Olimpic bisa matsayin siyasa.

A ranar 9 ga wannan wata, a lokacin da kasar Brazil ta yi tunawa da rana cika shekau 60 da bayar da sanarwar hakkin dan Adam, sakataren musamman na hakkin Dan Adam na kasar Mr Paul Vannuchi ya bayyana cewa, kasar Brazil ba za ta yi adawa da wasannin Olimpic ba, duk saboda shi ne kasaitatten taro na duk duniya. Wasannin Olimpic sun gabatar da shawarwari shimfida zaman lafiya, sun ba da taimako ga kasashe daban daban na duniya da su daidaita hargitsi ta hanyar yin tattaunawa.

A ranar 9 ga wannan wata, bayan da firayim ministan kasar New Zeland ya kammala ziyara a kasar Sin, sai ya bayyana cewa, kasarsa ba ta iya yin adawa da wasannin Olimpic na birnin Beijing ba, jama'ar kasar kuma suna sa ran alheri ga 'yan wasan kasar da za su halarci gasar wasannin Olimpic na birnin Beijing don su sami sakamako mai kyau.

Kwanan baya, tsohon firayim ministan kasar Jamus Helmut Heinrich Waldemar Schimidt ya karbi ziyarar da mujallar mako mako ta "Die Zeit" ta kasar Jamus ta yi masa, inda ya nuna kiyayya ga adawar da aka yi wa wasannin Olimpic na Beijing, kuma ya nuna kiyayya ga mayar da wasannin motsa jiki bisa matsayin siyasa.(Halima)