Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 10:46:05    
Shugabar Argentina ta nuna fatan alheri ga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Ran 10 ga wata, agogon wurin, shugabar kasar Argentina CristinaFernandez de Kirchner ta bayyana cewa, tabbas ne aikin mika wutar yolar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Buenos Aires zai ci nasara, a sa'i daya kuma ta nuna fatan alheri ga birnin Beijing da ya shirya gasar cikin nasara.

Cristina Fernandez ta fadi haka ne yayin da take ganawa da jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Argentina a fadar shugaba a wannan rana.

Fernandez ta ce, aikin mika wutar yola da za a yi a ran 11 ga wata a Buenos Aires zai kara zurfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen nan biyu, kuma zai sada zumunta da zaman lafiya. Wannan a karo na farko ne da wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta zo kasar Argentina, jama'ar kasar suna darajanta iznin sosai da sosai. Gwamnatin kasar za ta nuna babban goyon baya ga aikin. (Jamila Zhou)