Ran 10 ga wata, kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar da wani bayani mai taken "Kabilar Tibet kabila mafi muhimmanci ta jihar Tibet ce, wannan hakikanin abu ne da ba zai canja ba."
Bayanin ya ce, "Rahoton kididdigar bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta shekarar 2007" da hukumar kididdiga ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bayar ba da dadewa ba ya nuna mana cewa, yanzu, yawan mutanen kabilar Tibet ya kai fiye da miliyan 2 da dubu 500, ya kai kashi 95.3 cikin dari dake cikin adadin yawan mutanen jihar Tibet, sauransu mutanen kabilar Han da na sauran kananan kabilu ne. Ko shakka babu kabilar Tibet kabila mafi muhimmanci ta jihar Tibet ce, wannan hakikanin abu ne da ba zai canja ba, da kuma bai taba canja ba.
Bayanin yana ganin cewa, sakamakon lisafta ya shaida mana cewa, jitajitar da Dalailama ya baza a fili a duniya wai "kila ne mutanen kabilar Tibet za su zama mutane kalilan a gidansu" da kuma "Mutanen kabilar Han suna kara karuwa bisa babban mataki a jihar Tibet" ba su da tushe ko kadan, karya ce da ya yi don musunta hakikanin abu. Bisa tsarin cin gashin kan kabilu na kasar Sin, a kullum kabilar Tibet kabila mafi muhimmanci ce a jihar Tibet, wannan hakikanin abu ne da za a canja ba. (Jamila Zhou)
|