Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 21:59:33    
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin ta musanta shawarar da aka bayar ta wai yin "bincike na duniya", da "bincike na 'yancin kai" kan mumunan tashin hankali na Lasah

cri
Yau 10 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Jiangyu, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing cewa, akwai shawarar da aka bayar ta wai yin "bincike na duniya", da "bincike na 'yancin kai" kan lamarin duka da kwacewa da kone-kone da ya faru a birnin Lasah ba da dadewa ba, kasar Sin na ganin cewa, da farko ya kamata bangarori da kasashen da abin ya shafa su yi bincike kan wadanda ke tayar da mumunan tashin hakali da aka yi wa hukumomin kasar Sin sama da 10 da ke kasar Amurka da kasashen Turai.

Madam Jiangyu ta bayyana cewa, an taba samun barkewar tashin hankali a birane da yawa na kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka, da kasashen Turai. Amma, ra'ayoyin bainal jama'a na duniya sun nuna bambanci kan matakan magance lamari da wadannan kasashe suka dauka, da na kasar Sin ta dauka. Ta ce, idan an yi bincike kan masu tayar da lamarin a boye, da masakudinsu, to, za a fitar da abin gaskiya. (Bilkisu)