Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 16:20:42    
Alhakin rashin samun ci gaba a yunkurin tuntubawa yana kan wuyan mabiya Dalai Lama

cri

' Wajibi ne gungun mutane mabiya Dalai Lama su daina yin dukkan aika-aikan yin laifuffukan nuna karfin tuwo, da dakatar da gudanar da dukkan harkokin tada fitina da kuma shuka barna ga gasar wasannin Olympics ta Beijing a kuma danyen aikin janyo baraka ga kasar mahaifa, ta yadda za a kirkiro sharadin da ya wajaba na yin tuntuba da kuma shawarwari'. Mr. Sita, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin dunkulalliyar jam'iyyun siyasa ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a ranar jiya Laraba a nan birnin Beijing, inda ya kuma furta cewa, muhimmiyar manufa da gwamnatin tsakiya take aiwatarwa game da Dalai Lama, ita ce kofar yin shawarwari tsakanin gwamnatin tsakiya da Dalai Lama har kullum a bude take muddin Dalai Lama ya yi watsi da matsayin samun 'yancin Tibet, da dakatar da yin harkokin janyo baraka ga kasar mahaifa, da yin amincewa a fili a kan cewa Tibet wani kashi ne da ba za a iya balle shi daga yankin kasar Sin ba,kuma Taiwan wani kashi ne da ba za a iya raba shi daga yankin kasar Sin ba.

Sa'annan Mr. Sita ya furta cewa, lallai alhakin rashin samun ci gaba a yunkurin tuntubawa da shawarwari yana bisa wuyan mutane mabiya Dalai Laba. Muhimmin dalili shi ne wadannan mutane ba su nuna sahihiyar zuciya ba, kuma ba su yi watsi da matsayinsu na neman samun 'yancin Tibet ba haka kuma ba su daina yin aika-aikan janyo baraka ga kasar mahaifa ba. ( Sani Wang)