Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 16:07:32    
Kofofin watsa labarun Argentina suna sa ran alheri ga wutar wasannin Olympic

cri
Za a yi aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a ran 11 ga wata a birnin Buenos Aires wato babban birnin kasar Argentina. Wannan ne karo na farko da za a mika wutar yula ta wasannin Olympic a kasar, kafofin watsa labarun Argentina sun dora muhimmanci sosai ga wannan, suna sa ran alheri ga wutar wasannin Olympic. A sa'i daya kuma, sun ji takaicin tarzoma da aka tada don nuna adawa da wasannin Olympic a wasu kasashe.

Jaridar labarun Argentina ta bayar da labari a ran 9 ga wata cewa, za a mika wutar wasannin Olympic a birnin Buenos Aires, kuma ta amince da ra'ayin magajin birnin Buenos Aires wato mai da aikin mika wutar yula a wannan shahararren birnin Amurka ta kudu ya zama wani bikin dake cike da farin ciki.

Jarida mafi girma ta Argentina mai suna Mauricio Macri Clarin ta bayar da labarin dake da lakabi haka: wutar wasannin Olympic ta cigaba da kama hanya a ran 9 ga wata, inda ta ce, duk da cewar, an kawo fitina ga aikin mika wutar yula, amma za a kawar da ko wace wahala don cigaba da mika wutar yula a birnin Buenos Aires. Gwamnatin Buenos Aires ta yanke kudurin cewa, za ta shirya sosai don maraba da zuwan wutar wasannin Olumpic. (Lami)