Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 15:55:44    
Sauye-sauyen da musulmin kasar Sin suka samu wajen abubuwan sufuri

cri

Tun bayan da aka soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a shekaru 30 da suka wuce, Sinawa sun samu sauye-sauye wajen abubuwan sufuri, a lokacin taro a zaman farko na majalisar wakilai ta kasar Sin a karo na 10, wakiliyarmu ta kai ziyara ga wasu musulmi 'yan majalisar wakilai, inda suka tattauna kan sauye-sauyen da jama'ar kasar Sin suka samu wajen abubuwan sufuri tun shekaru 30 da suka wuce da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin.

'Dan majalisar wakilai malam Su Guangli, wani limami ne na masallacin Lanzhou ya gaya wa wakiliyarmu cewa, "Mu kan yi tafiya da kas a yau da shekaru 30 da suka wuce, daga baya kuma halinmu ya samu kyautattuwa, don haka muna da kudi don sayen kekuna."

Ya ce, a lokacin mutane su kan gamusu kan samu keke daya a iyalansu. A shekarar 1978, kasar Sin ta soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, saboda haka, tattalin arzikin kasar ya samu bunkasuwa, ta yadda aka soma yaduwar kekuna, tun daga lokacin, kasar Sin ta zama "Kasar kekuna" da ta yi suna a duniya.

A lokacin kuma, tikiti na bos yana da araha, amma ko da haka, ba kowa da kowa ke iya biya ba. Limami Su Guanglin ya waiwayi cewa, "Ko da ya ke a lokacin farashin tikiti na bos ba ya da yawa, amma saboda iyalinmu na fama da talauci a lokacin, don haka, ba mu dauka bos ba."

'Yar majalisar wakilai malama Ma Hanlan, wata ma'aikaciya ta hukumar yawon shakatawa ta gundumar Dongxiang ta jihar Gansu, ko da ya ke an haife ta a karni na 80, amma ta shaida halin bos irin maras zamani da ake ciki a da a nan kasar Sin. Ta ce, "A lokacin yarantakata, babu bos-bos da yawa, saboda haka, idan ka rasa wani bos, to za ka jira wani daban har dogon lokaci. Amma, yanzu bos-bos suna ta yi yawa, kana iya samun bos a ko wane lokacin da kake so."

Tun daga karni na 80 har zuwa karni na 90, wani abin sufuri daban, wato babur, ya shiga zaman rayuwar Sinawa. Mariya Matti, 'yar majalisar wakilai daga kabilar Kirgiz ta jihar Xinjiang ta gaya wa wakiliyarmu cewa, baburnta a da na man dizal ne, daga baya kuma, babura da yawa sun zama na wutar lantarki, lallai an soma mayar da hankali kan kiyaye muhalli.

A kasar Sin da ke tsakanin karni na 70 zuwa 80, abubuwan sufuri kamar jiragen kasa, da na sama ba su samu yaduwa kamar yanzu ba. Malam Bai Shangcheng, 'dan majalisar wakilai na kabilar Hui daga jihar Ningxia ya ce, "A shekarar 1979, a karo na farko ne na shiga jirgin kasa, don haka, na yi mamaki sosai."

Kan maganar shiga jirgin sama a karo na farko da ta yi, Halitan Nur Maimaiti ta kabilar Khazak, tana jin farin ciki sosai, ta ce, "A shekarar 1982, na je birnin Beijing don yin aiki, wannan ne karo na farko da na shiga jirgin sama, bayan da jirgin sama ya tashi, na ji kamar ina tashi cikin iska har ma na kusan taba sama."

Bisa kara ciyar da yunkurin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje gaba, da kuma bunkasuwar tattalin arziki a nan kasar Sin, abubuwan sufuri kuma suna ta samun sauye-sauye a kwana a tashi. Bayan da aka shiga karshen karni na 80 zuwa farkon karni na 90, motocin da jama'a suke da su sun soma yaduwa, tun daga karshen karni na 90 kuma, motoci sun riga sun shiga gidajen farar hula, wato ke nan, kasar Sin tana zaman "Kasar motoci" daga "Kasar kekuna" a hankali a hankali. Malam Wan Qiusheng, wani 'dan kabilar Hui daga jihar Shandong, ya gaya wa wakiliyarmu cewa, "A da, mutane su kan yi tafiya da kenuna, kuma da kyar ake iya samun babura, amma yanzu, na riga na canja motocina sau da yawa."

Malam Wan Qiusheng, abin koyi ne wajen raya sana'o'i cikin nasara bisa manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yanzu yana da kamfaninsa, dukiyoyinsa na da darajar kudin Sin sama da RMB biliyan 2. Ya ce, "Idan babu manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, to, ba zan iya kafa kamfanina ba."

Bayan da aka soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, musulmin da suka samu wadatuwa ta hanyar raya sana'o'insu kamar malam Wan Qiusheng, suna da yawa. Yanzu, tattalin arziki na kasar Sin ya samu bunkasuwa, kuma an samu sauki wajen sufuri, kazalika kuma, jama'a sun samu wadatuwa, saboda haka, musulmin da ke fatan cimma burinsu na yin aikin hajji a Makka, su ma suna ta yi yawa. Yin aikin hajji, wani darasi ne daga manyan darusa guda biyar na musulunci, don haka, dukkan musulmi na fatan tafi Makka. Tun bayan da kasar Sin ta farfado da aika da kungiyoyin yin aikin hajji a shekarar 1979, a ko wace shekara musulmin kasar Sin suna iya yin darasinsu na yin aikin hajji a Makka, kuma yawansu yana ta karu. Malam Su Guanglin ya gayawa wakiliyarmu cewa, ya riga ya je Makka don yin aikin hajji a shekarar 2006, amma a da yin aikin hajji ba wani abu mai sauki ba ne. Ya ce, "Akwai wuya da ake tunani da halin yin aikin hajji da ake ciki a da, a kan gama wannan darasi cikin dogon lokaci har fiye da shekara daya, saboda ba mu samu sauki ba wajen sufuri. A lokacin, tilas ne mu tashi daga birnin Beijing, amma yanzu muna iya tashi daga garinmu."

Lallai sauye-sauyen da aka samu wajen abubuwan sufuri, sun bayar da sauki sosai ga jama'a. A birane kuma, tsarin sufuri ya fi samu bunkasuwa. Malam Wang Xiaoke, 'yar kabilar Hui daga birnin Beijing ta ce, "A da, gwamnatinmu ta fi yin la'akari da bayar da sauki ga jama'a wajen tafiyarsu, amma yanzu, ta kara mayar da hankali kan sassauta cunkoso. Bisa bunkasuwar tattalin arziki, yawan motoci kuma yana ta karuwa. A shekarar da ta wuce, gwamnatin birnin Beijing ta rage farashin tikiti na abubuwan sufuri na jama'a, don kara kwarin gwiwa ga jama'ar birnin da su shiga abubuwan sufuri, ta yadda aka ba da amfani mai yakini kan sassauci matsalar cunkoso."

Bayan haka kuma, malama Wang Xiaoke ta ce, yanzu yawan motocin da jama'a ke da su suna ta yi yawa. Amma, za a bude wasannin Olympic na Beijing ba da dadewa ba, saboda haka, tana fatan a lokacin, mazaunan birnin Beijing za su zabi abubuwan sufuri na jama'a, amma ba motocinsu ba, don kafa wani muhallin sufuri mai kyau ga birnin Beijing.