Ran 9 ga wata da dare, agogon wurin, jirgin saman musamman mai lambar "wutar yula ta gasar wasannin Olympic" ya tashi daga birnin San Francisco na kasar Amurka zuwa tasha ta bakwai ta aikin mika wutar yula a kasashen waje wato Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina.
Ran 9 ga wata, agogon wurin, bayan da mai mika wutar yula na biyu ya fara mika wutar yular, bangaren da abin ya shafa na birnin San Francisco ya tsai da cewa, za a yi amfani da hanya ta biyu saboda dalilin kwanciyar hankali, a sanadiyar haka, hanyar mika wutar yular a birnin ta ragu, har ta kai rabin tsawon hanya ta farko kawai. Don nuna biyayya ga hukumar kasar Amurka, kungiyar mika wutar yula ta birnin Beijing ta yarda da wannan kuduri, a karshe dai, aikin mika wutar yular ya gudana lami lafiya a birnin.
Ran 11 ga wata, za a yi aikin mika wutar yular a birnin Buenos Aires na kasar Argentina. (Jamila Zhou)
|