Jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta da ke arewa maso yammancin kasar Sin tana da kasa makekiya, yawan fadinta ya kai kashi daya cikin kashi 6 na yawan fadin kasar Sin. Amma abun bakin ciki gare mu shi ne, wurin nan na da hamada mai fadi sosai, wanda ya kai kashi 60 cikin dari ko fiye bisa na yawan fadin hamadan kasar Sin. Ta hanyar kokarin da masu kyautata sauruka suka yi daga zuri'a zuwa zuri'a , ya zuwa yanzu, biranen da ke kara zama koriya shar suna kafuwa a hamadar nan. Birnin Shihezi da ake kiran shi lu'u-lu'un hamada yana cikinsu . To ga wasu abubuwan da za mu bayyana dangane da mutanen da ke zama a wurin.
Kafin shekara daya da ta wuce, mr Patrick Wallace da matarsa da suka zo daga kasar Amurka sun je aiki a birnin Shihezi, suna aikin koyarwa a wata jami'ar wurin. Kodayake ba su dade da zama a wurin nan ba, amma lokacin da manema labaru suka yi hira da su, sai suka bayana musu cewa, akwai kauna a tsakaninsu da wurin nan. Mr Wallace ya bayyana cewa,birnin nan birni ne da ke cike da launi koriya shar. A ko'ina da ka sa kafa , za ka iya ganin ciyayi da bishiyoyi da yawa. Idan dare ya yi, za a iya ganin taurari. A yanayin hunturu, ana kankara mai taushi kuma mai launin fari sosai, kai kankarar na da tsabta sosai da sosai. Muna kaunar Shihezi sosai,kuma muna son zama a wurin.
Yanzu, a kewayen birnin Shihezi, ana dasa bishiyoyi layi layi don hana kwararowar hamada, daga cikin fadin birnin da yawansa ya kai murraba'in kilomita 460 , yawan yankunan da ke cike mai launin koriya shar ya kai kashi 40 cikin dari ,wannan ba safai a kan ga irinsu ba a sauran biranen da ke arewa maso yammancin kasar Sin. Mutanen wurin sun bayyana cewa, a wurin nan, a lokacin yanayin bazara ya zo, a kan ga furanni da yawa, a yanayin rani, a kan samu inuwar bishiyoyi, a yanayin kaka, a kan samu 'ya'yan itatuwa, amma a yanayin hunturu, a kan ga launin koriya shar. Saboda sakamakon da ya samu wajen dasa bishiyoyi da ciyayi da sauran irinsu ne, birnin Shihezi ya sami lamba mafi kyau ta ba da kyakyawan misali ga kasashen duniya wajen kyautata muhallin mazauna a shekarar 2000 a birnin Dibai, a shekarar 2002, an kuma daukaka birnin don ya zama birnin lambuna bisa matsayin kasa.
Amma, ba a yi tsammani cewa, kafin shekaru fiye da 50 da suka wuce, birnin Shihezi shi ne karamin garin da ko'ina ake ganin fadamu ba, kuma sama ta cika da rairayi. Mutane sun bayyana wurin nan cewa, iska ta kan kado kananan duwatsu . Mataimakin direktan kwamitin kula da harkokin dasa bishiyoyi da ciyayi na birnin Shihezi mrRan Baiyu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 na karnin da ya wuce, tsofaffinmu sun gabatar da bukatunsu na hana iska da tsayar da kwararowar rairayi don kyautata muhallin zaman rayuwa, a shekaru 60 na karnin, an gabatar da shirin kafa birnin da ya zama birnin da ke da gonaki kamar yadda lambuna suke yi.A shekaru 80 na karnin, an gabatar da buri na gina birane don su zama na kiyaye halitta, a shekaru 90 na karnin, an gabatar da shirin gina birane don su zama irin lambunan bishiyoyi, amma yanzu, mun gyara shirye-shirye na da, muna raya birninmu sosai da sosai daga matsayin biyan bukatun mutane na yau da kullum kawai zuwa na kara kyau sosai.
A cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, gwamnatin wurin ta yi kokarin ba da taimako ga tsara manufofi da samar da kudade wajen dasa bishiyoyi da ciyayi da sauran irinsu a cikin birnin, a cikin 'yan shekaru uku da suka wuce, yawan kudaden da gwamnati ta ware ya kai kudin Sin Yuan miliyan 300.
Da ganin birnin da su kansu suka gina, mutanen birnin Shihezi sun yin alfahari sosai cewa, Shihezi ya sami manyan sauye-sauye, a da, wurin ba ya da hanyoyin motoci, kuma gidajenmu dukka bukkoki ko soraye ne, amma yanzu yana samun bunkasuwa da saurin gaske, birnin na da filayen wasa da na yin wake-wake, kai yana da kyaun gani sosai da sosai. Ya jawo sha'awar mutane da yawa don su je aiki da zaman rayuwa a wurin. Daga cikinsu, ba ma kawai da akwai tsofaffin masu yin aikin kyautata sauruka da zuri'arsu ba, hatta ma da akwai mutanen da suka zo daga sauran wuraren kasar Sin, har ma da akwai mutane kamar su mr Wallace da matarsa da sauransu da suka zo daga kasashen waje, suna kaunar birnin nan mai launin kore da ke cikin hamada, kuma suna farin ciki da zaman rayuwarsu a wurin.
|