Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 12:52:46    
An ce, mutane kalilan masu jawo baraka ga al'umma sun tayar da hargitsi a yankin Gannan ta jihar Gansu

cri

Ran 9 ga wata, mukadashin shugaban yankin Gannan ta kabilar Tibet mai cin gashin kanta na jihar Gansu dake yammacin kasar Sin Mao Shengwu ya gaya wa manema labarai a birnin Hezuo na jihar cewa, mutane kalilan masu jawo baraka ga al'ummar kasa ne suka tayar da hargitsi a Gannan.

Mao Shengwu ya ce , madugun 'yan tawaye sun daure zane siriri mai launin baki a kansu da kuma hannunsu, wannan ya nuna mana cewa, sun tayar da tarzoma bisa shirin da suka tsara. Irin wannan hargitsi shi ma ya auku a wasu gundumomi da kauyuka na yankin Gannan. Ba ma kawai masu neman 'yancin kan Tibet sun yi cudanya tsakaninsu a cikin gidan kasar Sin ba, har ma sun yi cudanya da masu jawo Baraka na kasashen waje.

Mao Shengwu ya ce , Bayan aukuwar tarzomar, hukumar kiyaye kwanciyar hankali ta kasar Sin ta kai bugu ga ayyukan laifin bisa doka, kuma an shawo kan halin yadda ya kamata. A halin da ake ciki yanzu, halin da yankin Gannan yake ciki yana zaman karko, zaman rayuwar jama'ar yankin na yau da kullum shi ma yana tafiya kamar yadda ya kamata. (Jamila Zhou)