Jaridar da ake kira ' The People's Daily' ta kasar Sin ta buga wani jawabin da wani mai yin sharhi ya rubuta dake da lakabin haka ' Ainihin zuci a karkashin lullubin halin kirki'.
Bayanin ya ce, a idon wassu mutane daga bangarorin kasa da kasa, Dalai Lama yana mai mutunta zaman lafiya da kyamar nuna karfin tuwo; Ban da wannan kuma, a idon wassu mutane mabiya addinai wadanda ba su san ainihin lamari ba, shi Dalai mai nuna halin kirki ne.
Bayanin ya kuma yi nuni da cewa, ko a fannin kirkiro matsalar nuna karfin tuwo da hura wutar yin haka ko ma a fannin yin sambatun banza cewar wai " kafa babban yankin Tiber" da " gudanar da harkokin Tibet cikin cin gashin kanta sosai da kuma " bin hanyar tsaka-tsaka", Dalai Lama ya yi haka ne da zummar neman 'yancin Tibet da kuma janyo baraka. Wasu mabiya Dalai sun yi ikirarin cewa wai " za su sake mayar da 'yancin Tibet komai sadaukarwa" kuma " za su sanya gwagwarmaya ta neman cikakken 'yancin Tibet. Wannan shi ne ainihin burin Dalai wanda ke sanye da lullubin " halin kirki". ( Sani Wang )
|