Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 10:53:44    
Kasar Sin ta bukaci tsirarrun mutanen majalisar dokoki ta kasar Amurka da su dakatar da kawo fitina ga wasannin Olympic da aikin mika wutar yula, in ji kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta amsa tambayoyin da manema labaru suka yi mata kan sanarwar da shugabar majalisar dokoki ta kasar Amurka Pelosi ta bayar game da mika wutar yula a birnin San Francisco a ran 9 ga wata, inda ta furta cewa, bangaren Sin ya bukaci tsirarrun mutanen majalisar dokoki ta kasar Amurka da su dakatar da kawo fitina ga wasannin Olympic da aikin mika wutar yula.

Madam Jiang Yu ta furta a nan birnin Beijing cewa, aikin mika wutar yula a birnin San Francisco, muhimmin lamari ne a tsakanin Sin da Amurka, duk jama'ar kasashen biyu suna fatan za a gudanar da aikin cikin lumana. Tsirarrun mutanen majalisar dokoki ta kasar Amurka sun yi kira da a kawo fitina ga aikin mika wutar yula a birnin San Francisco a fili, wannan abin halin rashin kirkin dan Adam ne , ko shakka babu, jama'ar kasar Sin da mutane masu hali na gari na kasashen duniya za su yi bakin ciki sosai gare shi.

Hakazalika, Madam Jiang Yu ta ce, aniyar kasar Sin da jama'ar kasashen duniya wajen yin wasannin Olympic na Beijing cikin nasara ba za ta canja ba, ba wanda ke iya tsayar da bunkasuwar kasar Sin. Bangaren Sin ya bukaci tsirarrun mutanen majalisar dokoki ta kasar Amurka da su dakatar da kawo fitina ga wasannin Olympic da aikin mika wutar yula nan da nan.(Lami)