Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 10:47:18    
Jaridar 'Macao Daily' ta zargi aikin hana mika wutar yula da karfin tuwo

cri

Ran 9 ga wata, jaridar 'Macao Daily' ta buga wani bayanin edita inda ta zargi lamarin hana mika wutar yular gasar wasannin Olympic da ya auku a London da Paris kwanakin baya. Bayanin ya yi nuni da cewa, masu neman 'yancin kan Tibet da rukunin nuna kiyayya ga kasar Sin na duniya sun sake nuna mana ainihin halinsu na son nuna karfin tuwo, aikinsu kalubale ne da suka yi wa dukkan jama'a masu kishin wasannin Olympic da zaman lafiya a duk duniya baki daya, ko shakka babu ba za su cim ma burinsu ba.

An samu labara cewa, a farkon watan Mayu, za a mika wutar yular a Macao. Bayanin editar ya kara da cewa, kodayake masu neman 'yancin Tibet ba za su sami goyon baya a Macao ba, amma birnin Macao birni ne mai bude kofa ga kasashen duniya, shi ya sa kila ne za a hana aikin mika wutar yular, saboda haka, kamata ya yi hukumar Macao da mazauna birnin su mai da hankali kan wannan, kuma su dauki matakan da suka wajaba don tabbatar da aikin mika wutar yular a Macao lami lafiya. (Jamila Zhou)