Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 22:04:40    
'Yan kabilar Zhuang da ke jihar Guangxi sun yi murnar bikin gargajiya na "ran 3 ga watan Maris"

cri
A ran 8 ga wata a babban filin ciyayi da ke gabashin garin Wuming na jihar Guangxi na kasar Sin, an buga ganguna don fara bikin rera wakoki na "ran 3 ga Maris" na gundumar Wuming wato garin kabilar Zhuang na kasar Sin, 'yan kabilar Zhuang fiye da dubu 10 da bakin da suka zo daga sauran wurare masu nisa sun tada murya sama suna rera wakoki domin murnar wannan gagarumin biki.

Kabilar Zhuang wata kabila ce wadda ta fi yawan mutane daga cikin kananan kabilun kasar Sin, wato yawan mutanenta ya kai fiye da miliyan 19, daga cikin su kuma da akwai mutane fiye da miliyan 16 wadanda suke zama a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta. Jama'ar kabilar Zhuang sun kware wajen rera wakoki, rera wakokin tudu da saurarar wakokin da kuma yin bikin rera wakoki duk wadannan ayyuka sun zama babban taken zamar rayuwar 'yan kabilar Zhuang wanda ba zai canja ba har abada. (Umaru)