Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 21:51:11    
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya

cri

Yau a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya gana da shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya, Mr.Jacques Rogge.

Mr.Wen Jiabao ya ce, wasannin Olympics da za a gudanar a shekarar da muke ciki a nan birnin Beijing kasaitaccen biki ne na jama'ar duniya baki daya. Yanzu ana mika wutar wasannin Olympics a duk duniya. Wutar wasanin Olympics alama ce ta zaman lafiya da zumunta da cigaba da kuma haske, wadda ke wakiltar fatan alheri na 'yan Adam ga kyakkyawar makoma. Sin tana da imanin cewa, wutar wasannin Olympic wadda ta kasance ta 'yan Adam baki daya ba za ta mutu ba.

Daga nasa bangaren kuma, Mr.Rogeg ya ce, kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya na nuna yabo sosai ga kokarin da kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing ya yi wajen gudanar da wasannin Olympics yadda ya kamata, kuma danka wa Sin nauyin gudanar da wasanni Olympics kuduri ne na daidai. Kamar yadda ya saba yi, kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya zai ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Sin wajen gudanar da wasannin Olympics. Bayan haka, Mr.Rogge ya yi fatan za a ci gaba da mika wutar wasannin Olympics a duniya yadda ya kamata, kuma yana da imanin cewa, gwamnatin kasar Sin na iya daidaita wasu matsalolin da suka taso.(Lubabatu)