Yau Laraba, Mr Qiangba Puncog, shugaban jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, jiharsa ta yi shiri sosai na mika wutar wasannin Olympic a jihar, tabbas ne, za a mika wutar wasannin Olympic lami lafiya kuma tare da cikakkiyar nasara.
A gun taron watsa labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, Mr Qiangba Puncog ya ce, mika wutar wasannin Olympic a jihar Tibet, alfahari ne ga jama'ar Tibet kuma nauyi ne da ke sauke bisa wuyansu. Jama'ar kabilu daban daban na jihar suna nuna cikakken goyon baya ga wannan. Kasar Sin tana cike da imani wajen tabbatar da mika wasannin Olympic a jihar Tibet lami lafiya kuma tare da cikakkiyar nasara. (Halilu)
|