Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 16:14:33    
Yawan kudin shiga da manoma da makiyaya a jihar Tibet ta kasar Sin suka samu sun karu sosai

cri

Bisa labarin da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya samu daga hukumar kula da aikin noma da na kiwon dabbobi ta jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin a yau Laraba, an ce, a cikin shekarun nan biyar da suka wuce, jihar ta kashe kudin Sin Yuan biliyan 2.3 wajen yin manyan ayyukan noma da na kiwon dabbobi, don haka an kara kyautata halin da manoma da makiyaya ke ciki a jihar dangane da aikin samar da kayayyaki da zaman rayuwa.

Bi da bi jihar Tibet ta gudanar da manyan ayyuka daban daban domin kiyaye filayen ciyayi da kyautata gonakin noman alkama iri na Tibet da kiwon dabbobi da sauransu. Haka kuma an yi ayyukan gina wuraren gas da ake samu daga tarin shara a kauyukan gundumomi 23 na jihar, ta haka yawan manoma da makiyya wadanda ke amfani da irin wannan gas ya wuce dubu 70. Ta hanyar yin wadannan manyan ayyuka, an kyautata halin da manoma da makiyaya ke ciki sosai game da samar da kayayyaki da zaman rayuwa.

An labarta cewa, matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane manomi da makiyayi a jihar Tibet ya samu a ko wace shekara ya wuce kashi 10 har cikin shekarun nan biyar da suka gabaa. (Halilu)