Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 16:10:19    
Kasar Sin ba za ta canja manufarta game da bude kofa ga kafofin watsa labaru na kasashen waje ba

cri

Jiya Talata, a birnin Beijing, yayin da Malam Wang Pijun, jami'in ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin yake bayyana wa hafsoshin soja sama da 70 na kasashe sama da 50 a kasar Sin hakikanin lamarin da ya auku a jihar Tibet ta kasar dangane da kai farmaki kan jama'a da farfasa kayayyaki da wawashe su da kuma sa wurare wuta, ya ce, gwamnatin kasar Sin ba za ta canja manufarta ba game da bude wa kafofin watsa labaru na kasashen waje kofa domin labaru marasa gaskiya da wasunsu kalilai suka bayar a kan wannan lamari.

Malam Wang Pijun ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana ba da kwarin gwiwa ga kafofin watsa labaru na kasashen waje da su kara yin ma'amala da hukumomin kasar da abin ya shafa, don kara fahimtar juna da inganta aminci da hadin kai, ta yadda za su kara yin abubuwa masu yawa don kara kawo fahimtar juna da dankon aminci a tsakanin jama'a, kuma su rage yin abubuwa wajen tunzura mutane da yada jita-jita.

A ran 14 ga watan jiya, tsirarrun masu laifi sun tayar da tarzomar kai farmaki kan jama'a da farfasa kayayyaki da wawashe su da kuma sa wurare wuta a birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin, sun kashe mutane 18 da ba su ci ba su sha ba, sun ji wa mutane 382 raunuka, haka kuma yawan kudin hasarar da suka jawo wa kantuna da gidajen jama'a ya kai kudin Sin Yuan miliyan 250. (Halilu)