Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 15:51:32    
Ayyukan ma'amalar al'adu tsakanin kasar Sin da kasashen waje a shekarar 2007 sun yi yawan gaske

cri

A ranar 21 ga watan Nuwama na shekarar 2007, an yi bikin bude makon sinima na kasar Sirilanka a birnin Beijing, makon na da bambanci da na sauran makon sinima na kasashen Turai da Amurka, wato a makon, an nuna sinima da yawancinsu na da halayen musamman na fannin addini na kasar Sirlanka, saboda haka an kara fahimtar kasar.

A cikin wani sashin sinimar kasar Sirilanka mai suna "Uppalawanna" da aka nuna a makon sinimar kasar Sirilanka. An bayyana wani labarin soyayya mai ban tausayi, wato an bayyana cewa, wata kyakkyawar sista mai kyaun gani sosai ta shiga soyayya tsakaninta da wani malamin koyar da ilmin raye-raye, amma iyayen Uppalawanna sun ki yarda da soyayyarsu, a karshe dai abin bakin ciki ya faru. Sinimar tana bayyana labarin sannu a hankali tare da nuna halayen musamman na addini sosai.

Shekarar 2007 shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Sirilanka, kasashen biyu sun shirya ma'amala sau da yawa a kan al'adunsu. Jakadan kasar Sirilanka da ke wakilci a kasar Sin Mr He K. Amunugama ya bayyana cewa, ya yi fatan 'yan kallo na kasar Sin za su iya kara fahimtar kasar Sirilanka ta hanyar kallon sinimar kasar, ya bayyana cewa, mun zabi sinimar da za a nuna a kasar Sin cikin tsanaki sosai kuma cikin dogon lokaci duk domin 'yan kallo na kasar Sin. Sinimar farko da muka zaba ita ce sabuwar sinimar da kasar Sirilanka ta dauka ba da dadewa ba, ta hanyar sinimar, 'yan kallo na kasar Sin sun soma fahimtar kasarmu, amma muna fatan za mu kara nuna sinimar da kasar Sirilanta ta dauka don bayyana kasar ta hanyoyi da yawa, wadannan sinima sun bayyana abubuwa da yawa dangane da abubuwan da muke kauna ko muke yin adawa da su da sauransu dangane da al'adar gargajiyarmu.

A shekarar 2007, ma'amalar al'adu tsakanin kasar Sin da kasashen waje na da yawa sosai, kuma an shirya tarurukan shekarar al'adu tsakanin kasar Sin da kasashen waje da yawa, ta hanyar nuna fasahohi da makon sinima da tarurukan nuna wasannin wake-wake da kide-kide da sauran hanyoyi don kara fahimtar juna. A watan Afril na shekarar 2007, a birnin Beijing da birnin Shanghai da sauran birane 12 na kasar Sin , an shirya shagulgula fiye da 100 da ke da lakabi haka: yanayin bazara na ma'amalar al'adu tsakanin kasar Sin da kasar Faransa, sa'anan kuma, kasar Japan da kasar Korea ta Kudu su ma sun shirya aikace-aikace da yawa na nuna fasahohi da sinima da taron dandalin tattaunawa da sauransu, a cikin taron shekarar al'adun kasar Spain, an yi shagalin raye-raye da nunin sinima da nunin fasalolin da aka tsara kan kayayyaki na zamanin yau da hotunan da aka dauka da dai sauransu, wanda ke kokarin samun digiri na biyu na jami'ar koyar ilmin noma ta kasar Sin Mr Yang Ce ya bayyana bayan kallon nunin cewa, kodayake ban taba koyon ilmin fasahohi ba, amma bayan da na je kallon nunin zane-zane da wasu mutum mutumi, sai na yi mamaki sosai da sosai, a wani lokaci, zuciyarka tana bugawa, amma bayan da ka duba wadannan kayayyakin fasaha, sai hankalinka kwance yake yi, fasahohi na da mamaki sosai ga mutane.

Sa'anan kuma, kasar Sin ta shirya aikace-aikacen nuna al'adun kasar Sin a kasashen waje da yawa. Ban da wasannin kwaikwayo na gargajiya da aka yi, an kuma nuna sinima na kasar Sin a kasashen ketare da yawa. An bayyana cewa, a shekarar 2007, yawan kudaden da kasar Sin ta samu a fannin sinima ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2 wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

Zane-zane da samari masu zane-zane na kasar Sin suka yi tare da wasu mutum mutumin da aka sassaka sun kuma sami sakamako mai kyau a kauwannin kasashen ketare.

Za a shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008 a birnin Beijing na kasar Sin, birnin Beijing da sauran wurare na kasar Sin dukansu suna shirya aikace-aikacen yin ma'amalar al'adu a tsakanin Sin da kasashen waje , ta hanyar wadannan aikace-aikace, ba ma kawai an kawo wa kasar Sin fasahohin al'adu na kasashen waje ba, hatta ma fasahohin al'adu na kasar Sin sai kara yawa suke yi su shiga sauran kasashen duniya.(Halima)