Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 14:43:05    
Shirin Pentathlon na zamanin da a cikin gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri
Masu karatu, yanzu bari mu yi muku bayani game da shirye-shiryen gasar wasannin Olympic ta zamanin da. A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, akwani wani irin shirin musamman da ya hada da sassa 5, wato dogon tsalle da jefa faifan karfe da jefa mashi da gudu da kuma kokawa.

Ko da yake watakila mutane sun lakanci sunayen wadannan shirye-shirye 5 na gasar Pentathlon ta zamanin da, amma wasu daga cikinsu sun sha bamban da wadanda muka gani a yanzu, ga misali, wasan dogon tsalle. Wasan dogon tsalle na zamanin da ya sha bamban da na zamanin yanzu sosai. Da farko, in wani dan wasa ya yi tsalle, to, tilas ne kafafunsu su daidaita, in ba haka ba, ba zai iya samun maki ba. Sa'an nan kuma, 'yan wasa sun yi tsalle tare da kidan sarewa domin karfafa gwiwarsu da kuma samun sautin gudu mai kyau, in kidan ya kare, to, lokacin gasarsa ya kare. Ban da wannan kuma, tilas ne ko wane dan wasa ya yi tsalle tare da wani dutse ko kuma kayan daga nauyi irin na karfe mai nauyin kilogram 1.5 zuwa 4.5. Ko da yake a ganin masana masu nazarin tarihin wasannin motsa jiki na zamanin yau, yin tsalle tare da wani dutse ba ya da amfani ko kadan, amma mutanen kasar Girka na da suna ganin cewa, yin amfani da wani dutse ya iya kara motsin hannayen 'yan wasa, ta haka, sun iya kara samun karfin gudu, haka kuma ya iya kiyaye daidaituwa jikunan 'yan wasa domin fada a kan kasa da kyau.

Galibi dai wasan jefa faifan karfe na zamanin yanzu na kasancewar kayan tarihi da aka gada daga gasar wasannin Olympic ta zamanin da. Motsi da kuma fasahohin jefa faifan karfe sun yi daidai da na zamanin da. A can can can da, 'yan wasa su kan jefa duwatsu. Amma a sakamakon bulluwar kayayayyakin karfe, a karni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., karfe ya maye gurbin dutse, sai mun sami faifan karfe da muka gani a yau.

Mutanen Girka na da sun gano darajar mashi a sakamakon yake-yake masu yawa, shi ya sa sun koyar da yaransu fasahohin jefa mashi a makaranta, wajibi ne yara su iya jefa mashi da hannunsu na dama da na hagu a lokaci guda. Dimbin sigogin musamman na mashi iri daban daban da ake amfani da su a yanzu, aka gaje su daga gasar wasannin Olympic ta zamanin da.

Akwai babban bambanci a tsakanin wasan gudu na da da na yanzu, tsawon hanyar ya kai mita 192 kawai.

Wasan kokawa ya zama na karshe a cikin gasar Pentathlon na zamanin da a gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da. A ko wace kungiya, 'yan wasa su kan yi karawa sau daya kawai.

'Yan wasan Pentathlon na zamanin da su kan yi takara mai tsanani a tsakaninsu a cikin wasan gudu da dogon tsalle da jefa faifan karfe da jefa mashi da kuma kokawa daya bayan daya. Wanda ya fi samun lambawan a cikin wadannan sassa 5 zai zama zakara a karshe dai, amma in 'yan wasa 2 sun sami maki iri daya, to, su kan ci gaba da gasar, su yi kokawa a tsakaninsu domin zama zakara.(Tasallah)