Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 14:20:46    
Jami'ai da kafofin yada labarai na wasu kasashe sun kai suka kan ayyukan da aka yi don neman yi wa wasannin Olympics na Beijing zagon kasa

cri

A cikin kwanakin baya baya, wasu jami'ai da kafofin yada labarai na kasashen Japan da Rasha da Hungary da kuma Farasan sun kai suka kan ayyukan da aka yi na neman yi wa wasannin Olympics na Beijing zagon kasa da yin adawa da matakan da aka dauka na neman dakatar da wasannin Olympics na Beijing.

A ran 8 ga wata, shugaban majalisar wakilai ta DUMA ta kasar Rasha Gryzlov ya kai suka kan matakan da aka dauka na neman dakatar da wasannin Olympics na Beijing. Ya bayyana cewa "kamata ya yi a daidaita matsalar siyasa ta hanyoyi daban, kome zai faru, wasannin Olympics na Beijing za su gudana bisa shirin da aka tsara."

A gun taron manema labaran da aka shirya ran 8 ga wata a birnin Tokyo,babban sakatare na majalisar ministoci ta kasar Japan Machimura Nobutaka ya ce,wasannin Olympics na Beijing gaggaruman wasanni ne na motsa jiki, mutanen duniya baki daya suna jiran nasarar wasannin Olympics na Beijing.Sabili da haka zanga zanga da aka yi cikin rashin lumana ba al'amarin farin ciki ba ne.

Jaridar "mouvelles d'europe ta kasar Faransa ta buga bayanin edita ran 8 ga wata inda ta yi nuni da cewa wata muhimmiyar ka'ida dake cikin tunanin Olympics ita ce ta zarce tsarin siyasa da tunani da al'adu na al'ada da kuma launin fata. Sa siyasa a cikin harkokin wasani ya sabawa da tunanin Olympics. Bayanin editan ya ce shaidodi masu karin yawa sun tabbata cewa tsirarun masu neman jawo baraka na Tibet sun kirkiro tashin hankali a Lhasa da farko,sannan sun sha ta da fitina a kokarin da ake yi na mika wutar wasannin Olympics na Beijing, makasudinsu shi ne yi wa wasannin Olympics na Beijing zagon kasa. Idan a lamunta wadannan tsirarun mutane su ci karensu babu babaka,za a cin zarafin tunanin wasannin Olympics da burinsa.(Ali)