Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 21:34:19    
Labaru game da lamarin Tibet da mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

A ran 8 ga wata a ofishin kula da harkokin waje na ma'aikatar tsaro ta kasar Sin, jami'ai na sojoji fiye da 70 na ofishoshin jakadanci na kasashe fiye da 50 a kasar Sin sun saurari halin da ake ciki dangane da mummunan tashin hankali da ya faru a ranar 14 ga watan jiya a birnin Lhasa.

Wani jami'in ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta nuna wasu hakikanan abubuwa, wadanda suka bayyana cewa, rukunin Dalai Lama da 'yan a-ware na Tibet su ne suka yi kulle kullen lamarin ne. Ban da wannan kuma, ya ba da amsoshin ga tambayoyin da aka yi masa game da halin da ake ciki yanzu a jihar Tibet da kuma yadda manema labaru suke neman labaru a jihar.

An yi wata tambaya cewa, ko za a mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a jihar Tibet? Wannan jami'i ya ce, za a mika wutar a jihar Tibet bisa shirin da aka yi, a halin yanzu, gwamnatin jihar Tibet da sassan da abin ya shafa suna gudanar da ayyukan share fage domin karbar wutar yola.

Bisa labarin daban da muka samu, an ce, masu karanta shafin internet da yawa na gida da na waje sun kai suka sosai kan 'yan a-ware na Tibet da su lalata aikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)