|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-04-08 20:25:00
|
|
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta musanta maganar da Dalai Lama ya yi ta cewar, wai yana tsayawa kan "Tsakiyar hanya"
cri
A gun taron manema labaru da aka shirya a yau 8 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Jiang Yu ta musanta maganar da Dalai Lama ya yi a kwanan baya a "Takardar gaya wa 'yan uwa na Tibet", inda ya bayyana cewa, ba ya da nufin "neman 'yancin kan Tibet", amma yana tsayawa kan "Tsakiyar hanya". Madam Jiang Yu ta ce, Dalai yana wakiltar tsarin bayi na manoma, wanda ya hada da siyasa da addinai. Babu dimokuradiya, da 'yancin kai, da kuma hakkin bil Adam a karkashin wannan tsari, sai hakkin musamman na masu tafiyar da mulki kawai. Nufin "Tsakiyar hanya" da Dalai Lama ke nema, shi ne, komawa kan tsarin.
A waje daya kuma, madam Jiang Yu ta musanta maganar da Dalai Lama ya yi ta cewar, wai ba ya da nasaba da lamarin duka da kwacewa da kone-kone, wanda ya faru a birnin Lasah. Ta jaddada cewa, abin da Dailai Lama ya yi a kwanan baya shi ne, tayar da shirya lamari na nuna karfin tuwo a birnin Lasah. (Bilkisu)
|
|
|