Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:52:02    
Gaskiyar tarzomar da ta auku a Tibet ta sami martani sosai danga wajen masu sauraron CRI

cri
Kwanan nan, ta rediyonsa da shafunansa na internet ne, gidan rediyon kasar Sin, wato CRI, ya bayyana gaskiyar tarzomar da ta auku a birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin, wadda ta sami martani sosai daga wajen masu sauraronsa da kuma masu karanta shafunansa na internet a kasashe daban daban, kuma da yawa daga cikinsu sun turo mana wasiku da kuma buga mana waya, don yin Allah wadai da tarzomar tare kuma da nuna goyon baya ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka. Sun kuma bayyana cewa, ba su yarda da hada batun Tibet da wasannin Olympics na Beijing, kuma suna fatan Sin za ta gudanar da wasannin Olympics cikin nasara.

Ricardo Huerta, wani mai sauraron CRI a kasar Argentina yana samun fahimtar gaskiyar tarzomar da ta auku a Tibet daga filin musamman da aka kebe a shafin internet na harshen Spain na gidan rediyon kasar Sin, kuma ya rubuta a shafin cewa, na ji fushin neman balle Tibet daga kasar Sin da 'yan awaren Tibet suka yi. A ran 25 ga watan Maris da ya wuce, wannan mai sauraron ya kuma buga waya ga sashen Spain na gidan rediyon kasar Sin cewa,"tarzomar da ta auku a Tibet ta ba ni mamaki sosai, na taba zuwa kasar Sin har sau biyu, labaran da wasu 'yan hamayyar kasar Sin suka baza dangane da halin da Sin ke ciki bisa batun Tibet ba su sami gindi ba, kuma sun saba wa abubuwan da na gani. Yunkurin neman shafa wa kasar Sin bakin fentir da kaurace wa wasannin Olympics bisa tarzomar da ta auku a Tibet da wasu 'yan hamayyar kasar Sin da 'yan aware suke yi ba zai sami karbuwa ba."

Masu sauraron sashen harshen Italiya na CRI ma sun turo mana wasikunsu a kwanan baya, don bayyana kyamarsu ga aukuwar tarzoma a jihar Tibet. Mr.Zhang Jin, ma'aikacin sashen harshen Italiya ya bayyana cewa,"Bayan da ya sami labarin aukuwar tarzoma a Tibet, Giordano Marcheselli, wani tsohon mai sauraron sashen harshen Italiya ya buga mana waya nan da nan, don la'anci al'amarin da kuma bayyana bakin cikinsa. Ya kuma nuna goyon baya sosai ga matsayin gwamnatin Sin a kan al'amarin. "

Ban da wannan, Shahid Azmi, mai sauraron CRI daga kasar Indiya ya buga waya ga sashen harshen Indiya, inda ya yi Allah wadai da aukuwar tarzoma mai tsanani a Tibet da neman cimma mummunan burinsa da Dalai Lama ke yi bisa wasannin Olympics. Ya ce,"Ban yarda da tarzomar da ta auku a Tibet ba. Yanzu an sami manyan sauye sauye a Tibet, har ma an shimfida hanyar dogo a wannan wurin da ake kira kololuwar duniya, kuma zaman rayuwar jama'a ya inganta. Amma rukunin Dalai Lama ya yi biris da cigaban Tibet. Don neman jawo hankalin duniya, sun yi amfani da wasannin Olympics da za gudanar a birnin Beijing, sun tayar da tarzoma, don neman cimma burinsu na jawo baraka ga kasar Sin. Mu masu sauraro daga Indiya muna nuna rashin amincewa sosai. Da zuci daya ne muke fatan Tibet zai kara samun ci gaba, jama'arsa za su kara jin dadim zaman rayuwa. A ganina, duk wanda ke kaunar dan Adam da kasar Sin da wasanni da gaskiya da zaman lafiya, ba shakka zai nuna cikakken goyon baya ga wasannin Olympics na Beijing.

Sai kuma Mchana J.Mchana wanda ya zo daga kasar Tanzania, ya aiko mana Email cewa, dole ne shugabannin Sin da jama'arta su shawo kan halin da ake ciki a Tibet. Ina fatan jama'ar Sin ba za su yi kasa a gwiwa ba, a maimakon hakan, su ci gaba da share fage ga wasannin Olympics, kada dai 'yan awaren Tibet su cimma burinsu na lalata wasannin Olympics.(Lubabatu)