Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 16:42:58    
Sin ta sanar da shirin manyan ayyukan al'adu dangane da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008

cri

A ran 8 ga wata a birnin Beijing, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta shirya wani taron manema labaru, inda ta sanar da shirin manyan ayyukan al'adu da za a gudanar domin gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008.

Mai ba da taimako ga ministan al'adu Mr Ding Wei ya bayyana cewa, daga watan Maris zuwa watan Satumba na bana a birnin Beijing, za a gudanar da nagartattun shirye shirye da yawansu zai zarce 260, da kuma bukukuwan nune nune da yawansu ya kai kusan 160 da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 80. Masu fasaha na gida da na waje da yawansu zai zarce dubu 20 za su shiga cikin shirye shirye da bukukuwan nune nune. Wannan zai zama babban lamarin al'adu da ya fi girma bisa matsayinsa, kuma ya fi ba da kwarewa, kuma ya fi dogon lokaci da za a yi a birnin Beijing a shekarar bana.(Danladi)