A ran 8 ga wata a nan birnin Beijing, Madam Yan Jiangying, kakakin hukumar sa ido kan ingancin abinci da magani na kasar Sin ta bayyana cewa, daga ran 1 ga watan Mayu, dukkan magungunan da ke hade da magani mai sa kuzari dole ne a rubuta bayanin haka a kai wato "'yan wasan motsa jiki su mai da hankali kan wannan magani", im ba haka ba kada a sayar da su.
Madam Yan ta ce, daga watan Oktoba na shekarar da ta wuce, sassa da yawa na kasar Sin sun fara aikin musamman ta hanyar hadin gwiwa domin daidaita matsalar magani mai sa kuzari. A gun wannan aiki, sun gano kuma sun yanke hukunci kan masana'antu 18 da ke fitar da magunguna masu sa kuzari da masana'antu 14 da ke sayar da irin wadannan magunguna. (Umaru)
|