Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 14:57:58    
Fayaloli sun shaida cewa, Tibet yanki ne ba za a iya kebe shi daga kasar Sin ba

cri

A ran 7 ga wata, Mr. Yang Dongquan, shugaban hukumar ajiye fayaloli ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar bisa wasu fayalolin daular Yuan da suke da nasaba da yankin Tibet da hukumar ta bayar ga jama'a sun shaida cewa, yankin Tibet wani yanki ne da ba za a iya kebe shi daga kasar Sin ba.

Mr. Yang ya gaya wa manema labaru cewa, tun lokacin da, yankin Tibet wani yankin kasar Sin ne. A cikin shekaru fiye da 700 tun daga lokacin da kasar Sin take karkashin daular Yuan, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yi ta yin mulki kai tsaye a yankin Tibet. Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta nada jami'ai a yankin, kuma ta kafa mukaman jami'ai da hukumominta a yankin. Har yanzu ana iya karanta dukkan takardun da gwamnatocin tsakiya na dauloli daban-daban na kasar Sin suka samar wa yankin Tibet domin tabbatar da ikonsu na mulkin Tibet, ba su taba tsagaitawa ba.

Mr. Yang Dongquan ya bayyana cewa, wadannan fayaloli masu daraja suna kunshe da umurnoni da lambobin zinariya da na tagulla da sarkunan daulolin Yuan da Ming da Qing suka bayar wa yankin Tibet. Wadannan abubuwa sun shaida sosai cewa, gwamnatin tsakiya ta daular Yuan, wato yau da shekaru fiye da dari 7 da suka gabata, ta riga ta soma kafa hukumomin mulkin yankin Tibet da nada jami'ai a yankin. Wadannan fayaloli sun shaida cewa, ko shakka babu yankin Tibet wani yanki ne na kasar Sin tun lokacin aru aru da suka gabata.(Sanusi Chen)