An fara ayyukan mika wutar yular wasannin Olympic na Beijing na tasha na 5 a ran 7 ga wata bisa agogon wuri a birnin Paris na kasar Faransa, bayan da aka kau da fitinar da wasu masu neman 'yanci kan jihar Tibet suka yi, an gama ayyukan mika wutar.
An yi bikin fara mika wutar yula da karfe 12 da rabi da rana bisa agogon wurin a hasumiyar Eiffel, mai mika wutar yula na farko shi ne tsohon zakaran wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Faransa Stephane Diagana.
A kan hanyar mika wutar yula, an samu fitinar da wasu masu neman 'yanci kan jihar Tibet suka yi. Domin tabbatar da tsaro, kuma bisa abubuwan da kwamitin Olympic na duniya ya kayyade, tawagar mika wutar yula na kwamitin wasannin Olympic na Beijing ta yanke kudurin kashe wutar yula, sa'a nan an ajiye wutar yula cikin mota don cigaba da kama hanya.(Lami)
|