Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 13:49:00    
Wutar yolar wasannin Olimpic ta Beijing ta tashi zuwa birnin San Fransicco daga birnin Paris

cri
A ranar 7 ga wannan wata da dare, , jirgin sama na musamman da ke dauke da wutar yolar wasannin Olimpic ta Beijing ya tashi daga birnin Paris, hedkwatar kasar Faransa don zuwa birnin San Francisco, tasha ta 6 da za a mika wutar yola a kasashen waje.

A ranar 7 ga wannan wata da tsakar rana da karfe 12 da rabi, an soma mika wutar yolar wasannin Olimpic ta Beijing a wurin da ke gindin Effel Tower wanda shi ne ginin da ke iya alamanta birnin Paris. Aikin mika wutar yolar wasannin Olimpic ya kawar da tarnakin da 'yan aware na Tibet suka yi ta hanyar zanga-zanga, kuma ta hanyar mikawar da masu mika wutar yolar suka yi daya bayan daya, ya zuwa karfe 5 na wannan rana da yamma, an kammala mika wutar yolar a karo na karshe, sai wutar yolar ta sauka filin wasannin motsa jiki na Charlety.

A ranar 9 ga wannan wata, za a mika wutar yolar a birnin San Faransico.(Halima)