Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 09:47:52    
Ra'ayi maras gaskiya tsantsa bai iya mamaye gaskiya ba

cri
A ran 7 ga wata, kamfanin dillanci labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani sharhi, inda ya kai suka kan maganganu da shirin kudurin da madam Pelosi, shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka da tsirarrun 'yan majalisar suka yi a kwanan baya, wai sun yi kira ga gwamnatin kasar Sin da ta daina daukan matakan da take dauka a jihar Tibet, kuma ta yi hakikanin shawarwari da Dalai. Wannan sharhi ya ce, wadannan mutane sun kyale hakikanan abubuwa sun dauki irin wannan mataki, a hakika dai ba gaira ba dalili.

Wannan sharhi ya kara da cewa, ko shakka babu matakin da wadannan mutane, ciki har da madam Pelosi suka dauka yana mayar da baki fari. Tashe-tashen hankula da suka auku a Lhasa wata matsalar nuna karfin tuwo ce da rukunin Dalai ya shirya sosai, kuma ya tayar, wannan abin gaskiya ne da jama'ar wurin da masu yawon shakatawa na kasashen waje suka gani da idanunsu. Madam Pelosi da wasu mutane ba su yi tir da 'yan ta'adda da suka ta da hankali a birnin Lhasa ba, kuma ba su yi tir da rukunin Dalai da ya shirya tayar da laifin nuna karfin tuwo ba, amma sun yi wa gwamnati da jama'ar kasar Sin matsin lamba. Duk wadanda suke nuna adalci za su tambaye su, ina ka'idar gaskiya da suke bi?

A waje daya kuma, wannan sharhi ya ce, manufar da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan Dalai tana kasancewa a fili kamar yadda take bi a kullum. Da Dalai ya yi watsi da matsayinsa na neman 'yanci kan Tibet da daina matakan kawo wa kasar Sin baraka, kuma ya amince da cewa, yankin Tibet da yankin Taiwan yankuna ne da ba za a iya kebe su daga duk kasar Sin ba, gwamnatin kasar Sin tana son ci gaba da yin shawarwari tare da shi. Amma gwamnatin kasar Sin ba za ta ba da kai ga matsin lambar da aka yi mata ba. Kuma ba za ta yi rangwame ba ga dukkan yunkurin kawo wa kasar Sin baraka da lalata hadin guiwar da ke kasancewa a tsakanin kabilu daban-daban, irin wannan yunkuri ma ba zai samu nasara ba. (Sanusi Chen)