Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 13:46:30    
Bangaren kasar Sin ya kai suka sosai ga 'yan aware na Tibet da suka kawo barna kiri da muzu ga mika wutar yolar wasannin Olimpic

cri

A ranar 8 ga wannan wata a birnin Beijing, a lokacin da kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Jiangyu ta amsa tambayoyin da manema labaru suka gabatar dangane da barna da 'yan aware na Tbiet suka yi kiri da muzu ga mika wutar yolar wasannin Olimpic, ta bayyana cewa, da kakkausan harshe ne bangaren kasar Sin ya kai suka kan 'yan aware na Tibet da suka kawo barna kan mika wutar yola ta wasannin Olimpic.

Madam Jiang ta bayyana cewa, wasannin Olimpic na birnin Beijing kasaitattun wasannin motsa jiki ne na duk jama'ar duniya, wutar yolar wasannin Olimpic wutar yola ce ta jama'ar duniya. A ranar 6 da ranar 8 ga wannan wata, bisa karbuwa sosai da jama'ar kasar Britaniya da ta kasar Faransa suka yi ne, an riga an kammala dawainiyar mika wutar yolar wasannin Olimpic ta Beijing a birnin London da Paris.

Madam Jiang ta ci gaba da cewa, da harshe mai zafi ne bangaren kasar Sin ya kai suka ga 'yan aware na Tibet saboda sun yi biris da halin wasannin Olimpic da dokokin shari'a na kasar Britaniya da Faransa , sun kawo barna ga mika wutar yolar wasannin Olimpic kiri da muzu. Wannan danyen aiki ya kawo illa ga halin wasannin Olimpic mai muhimmanci, kuma kalubale ne da suka yi ga mutane masu kishin wasannin Olimpic na duk duniya. Bangaren kasar Sin ya amince cewa, kowane mutum ba zai iya hana halin wasannin Olimpic da tunanin shimfida zaman lafiya da sada zumunta da ci gaba wadanda wutar yolar wasannin Olimpic ke dauke da su.(Halima)